Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa ma’aikatarsa za ta fara horar da ‘yan jaridun soshiyal midiya kan sabbin hanyoyin yaɗa labarai da kuma amfani da fasahar zamani. Ministan ya bayyana haka ne a saƙon godiya da ya aika wa mahalarta taron farko da aka yi da ‘yan jaridun soshiyal midiya na Arewacin Najeriya a ranar Laraba a Abuja.
Ya bayyana jin daɗinsa kan yadda taron ya gudana, inda aka samu musayar ra’ayoyi da shawarwari masu amfani daga mahalarta. Ministan ya jaddada cewa irin wannan zaman za a ci gaba da gudanar da su kafin ƙarshen shekara.
Alhaji Idris ya kuma ce za a riƙa ɗaukar wasu daga cikin mahalarta taron don ba su horaswa ta musamman a kan fasahohin zamani ciki har ilimin ƙirƙirarriyar fasaha wato artificial intelligence, wanda ma’aikatar za ta shirya. Ya ƙara da cewa makamancin wannan taro za a shirya shi ga ‘yan jarida daga Kudancin Najeriya a nan gaba.