Yanƙurin Trump na Shigar wa Isra’ila yaƙi: Yadda hakan ya raba kan Jami’an Gwamnatinsa

Dsga Yusuf Kabiru
kabiruyusuf533@gmail.com
09063281016.

Akwai takurawa na soja da fasaha waɗanda ke ƙara nuna rashin iyawar Isra’ila na lalata cibiyoyin nukiliya na Iran (kamar su Natanz da Fordo da aka gina a ƙarƙashin duwatsu zuwa zurfin mita 800, kamar yadda shugaban hukumar makamashin nukiliya ya bayar da rahoto).

Wannan saboda Isra’ila ba ta da bam na GBU-57 (Bunker Buster) da jiragen yaƙi masu ɗauke da makamai masu girma (B-1, B-2) da ake buƙata don ɗaukar su. Har ma Amurka kanta tana fuskantar matsaloli wajen amfani da jiragenta masu ɗaukar makamai masu girma; domin hakan yana buƙatar sanar da Rasha kafin a kai hari bisa ga yarjejeniyar START 3, wannan kuma yana kawar da abin mamaki. An yi wa waɗannan jiragen takurawa mai tasiri a lokutan kai hare-hare kan ƙungiyar Houthi, wanda ya rage tasirinsu kuma ya tilasta wa Amurka janyewa daga sararin saman Yemen. Waɗannan ƙahon zugar ya fito ne daga Sin da Rasha waɗanda ke gwada tsarin tsaron kansu a kan Amurka don shirye-shiryen yaƙin duniya na uku da ake tsammanin zai ɓarke a kowane lokaci.

Ko da bam din GBU-57 (wanda zai iya tono ƙasa har mita 60 kawai) bai isa ya lalata cibiyoyin da ke zurfin mita 800 ba, kuma yana buƙatar tsawaita aiki tuƙuru kafin tabbatuwar hakan.

Haka nan, akwai haɗarurruka masu girma da Amurka ba za ta yarda da su ba, waɗanda suka haɗa da mummunan martanin da Iran za ta yi da kuma ikonta na kai hari kan sansanonin Amurka masu mahimmanci kamar sansanin Al Udeid a Qatar, da sansanin nukiliya a Turkiyya (inda Amurka ke ajiye makamai nukiliya guda 50 na nau’in B61). A cikin waɗannan sansanonin biyu akwai kusan sojojin Amurka dubu 60, da sauran sansanonin da ke Iraƙi, Bahrain, UAE, Kuwait, Saudiyya… duk za su zama abin harba makamai masu linzami na Iran.

Idan Amurka ta shiga yaƙin, za ta fuskanci barazana masu tsanani na tattalin arziki, mafi mahimmanci su ne rufe mashigar Hormuz da Iran za ta yi, da kuma rufe mashigar Bab al-Mandab da Houthi za su yi; wannan zai iya haifar da hauhawar farashin man fetur sama da dala 500 a kowace ganga, wanda zai jawo mummunar asara ga tattalin arzikin Amurka da kamfanoninta. Amma ba wannan kawai ke damun Amurka ba; tana da tsoron tashin makaman nukiliya, domin rahotannin leƙen asirin sun nuna cewa Iran tana da makaman kare dangi kamar bam mai gurɓata (dirty bomb) wanda ke da karfin bam din nukiliya da aka jefa a Hiroshima, da kuma bayanan da ba a tabbatar da su ba game da sayen bam din nukiliya guda uku daga Koriya ta Arewa. Har ila yau, Sin ta ba Iran tsarin yaƙi na intanet (warfare electronic) mai amfani da fasahar 6G, wanda ke iya takura jiragen sama na ɓoye (stealth) da kuma ƙirƙirar maƙasudai na bogi sama da 3600. Bugu da ƙari, ga shigar hannun Iran da kawayenta cikin yaƙi, da kuma barazanar da hakan ke haifarwa ga muradun Amurka, balle ma yuwuwar bala’in tauraron ɗan adam saboda yaduwar radiyo a yankin.

YADDA YUNƘURIN SHIGA YAƘIN YA FARRAƘA JAMI’AN GWAMNATIN TRUMP

Bugu da ƙari, akwai rarrabuwar kawuna a cikin gwamnatin Amurka; manyan shugabanni (kamar shugaban CIA, shugaban hafsoshin soji, jami’in sansanonin Amurka a Gabas ta Tsakiya, da shugabar hukumar leƙen asirin ƙasa Tulsi Gabbard) suna adawa da kai hari kan Iran saboda tsoron mummunan martaninta.

YADDA YAƘIN NAN YA ƘARA HAƊA IRANIYAWA A CIKIN GIDA

Kuma fatan Isra’ila da Amurka da kawayensu na kawo canji a cikin Iran bayan kashe shugabanninta da kai hare-hare sama ya warware; domin waɗannan abubuwan sun ƙara ƙarfafa haɗin kan al’ummar Iran (ciki har da masu adawa) ga gwamnati a waje da cikin ƙasa, a’a akasin haka ya faru: matsin lamba daga al’ummar Isra’ila ya ƙaru, da kuma karuwar tsoron rugujewar yanayin cikin Isra’ila idan hare-haren Iran suka ƙaru kuma yaƙin ya ci gaba.

Saboda haka, mafi kyawun zaɓin Amurka shi ne matsa lamba don dakatar da yaƙin ta hanyar tattaunawa ko “ragewa sannu a hankali” na hare-haren tsakanin ɓangarorin biyu har sai sun kai ga rikice-rikicen da ba su da tasiri, musamman ma yadda Trump ya yi wa al’ummar Amurka alƙawarin a lokacin yaƙin neman zaɓensa na guje wa yaƙe-yaƙe masu tsada. Kuma mafi mahimmanci shi ne burinsa na sirri na samun lambar yabo ta Nobel ta zaman lafiya, saboda haka rashin shiga yaƙi da kuma sanya hannu kan yarjejeniyar nukiliya da Iran shi ne mafi kusanta. Amma Amurka za a iya tilasta mata shiga yaƙin kawai idan Iran ta dage kan lalata Isra’ila kuma ta ƙi duk wata mafita ga yaƙin ko shirin nukiliya.

Yusuf Kabiru Ɗan Jarida ne mai sharhi a kan siyasar gabas ta tsakiya

Za a iya samunsa a: kabiruyusuf533@gmail.com
09063281016.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *