Fasinja Ya Rasu a Jirgin sama na Ibom Air

Wani fasinja a cikin daya daga cikin jiragen Ibom Air ya rasu ranar Lahadi ana tsaka da tafiya a sama

A cewar labarin, fasinjan jurgin, wanda ya taso daga Legas zuwa Abuja ya kamu da rashin lafiya ne kimanin mintuna 20 bayan fara tafiyar.

Lamarin ya tsananta har matukin jirgin sai da ya kira tashar filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da gaggawa bayan an yi ma fasinjan agajin farko a cikin jirgin.

An samu labarin cewa filin jirgin ya shirya komai don kula da fasinjan lokacin sauka.

Saboda cunkoso da gujewar jinkiri, an ba jirgin izinin sauka a bangaren shugaban ƙasa na filin jirgin, inda ma’aikatan lafiya da motar asibiti suka tsaya jira.

Amma a lokacin saukar, wasu majiyoyi marasa tabbaci sun ce duk ƙoƙarin farfado da fasinjan ya gaza, kuma an kai shi asibiti.

Babu wata sanarwa ko tabbaci daga FAAN ko Ibom Air game da wannan lamari.

Duk ƙoƙarin tuntuɓar Ibom Air don jin martanin su game da lamarin bai samu nasara ba har lokacin wallafa labarin nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *