Najeriya tare da ƙasashe 144 sun kada kuri’a a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) domin ba wa Shugaban Falasɗinu, Mahmoud Abbas, damar yin jawabi ta bidiyo a babban taron Majalisar bayan Amurka ta ƙi ba da visa ga tawagarsa.
An kada kuri’ar ne a New York, inda aka samu ƙuri’u 145 na amincewa, ƙasashe biyar suka ƙi (ciki har da Amurka da Isra’ila), yayin da ƙasashe shida suka kaurace wa kaɗa kuri’ar.
Wannan matakin zai bai wa Abbas damar aiko da jawabin sa da aka riga aka ɗauka ta bidiyo, wanda wani wakilin Falasɗinu a New York zai gabatar a dakin taron. Haka kuma an amince a yi amfani da wannan tsari na jawabin bidiyo ko ta haɗin kai tsaye (live) a wasu muhimman taruka na MDD, amma a abin da ya shafi zaman majasar karo na 80 kawai.