Babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya, PDP ta sanar da korar ministan Abuja, Nyesom Wike, da wasu jiga-jigai daga cikinta, saboda abin da ta kira “yi wa jam’iyya zagon-ƙasa.”
Cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce ta ɗauki matakin ne domin kawo haɗin kai da ladabtarwa a jam’iyyar da kuma mayar da hankali ga zaɓukan 2027 masu zuwa.
Sauran mutanen da jam’iyyar ta kora sun haɗar da Samuel Anyanwu da Kamaldeen Ajibade da Ayo Fayose da Austin Nwachukwu da kuma wasu.
Sanarwar ta ce matakin ya samu amincewar mafiya rinjayen wakilan jam’iyyar da ke halartar babban taronta na ƙasa da ke gudana a birnin Ibadan na jihar Oyo.
BABU HANNUNA A KORAR WIKE, CEWAR GWAMNA FINTIRI
Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya nesanta kansa daga matakin da jam’iyyar PDP ta ɗauka na korar ministan Abuja, Nyesom Wike da wasu daga jam’iyyar.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinta X, Ahmadu Fintiri ya ce, ya yi imanin cewa babu abin da matakin zai haifar sai ƙara dagula jam’iyyar.
”Ni, Ahmadu Umaru Fintiri, gwamnan Adamawa ina son na bayyana ƙarara cewa na nesanta kaina daga wannan matsayi da PDP ta ɗauka na dakatar da Wike daga cikinta”.
Gwamnan ya ƙara da cewa ba zai goyi bayan duk wani mataki da zai ƙara jefa jam’iyyar cikin rikici ba.
”A matsayina na halastaccen ɗan jam’iyya, ina goyon bayan zaman lafiya da kwanciyar hankalin jam’iyyarmu, don haka ba zan goyi bayan duk wani mataki da zai wargaza ta ba”, in ji Fintiri.
Gwamnan ya kuma yi kira ga jam’iyyar ta rungumin hanyoyin sasanci domin warware duka matsalolin da jam’iyyar ke fuskanta.
