Daga Abdullahi Richifa
“A madadin ɗaukacin ma’aikatan kamfanin MIZANI PUBLICATIONS, mai buga jaridar ALMIZAN, muna miƙa saƙon ta’aziyyarmu ga Kakakin Gwamnan jihar Zamfara, Hon. Idris Suleiman Bala game da rasuwar mahaifinsu Marigayi Malam Sulaiman Mika’il Abdullahi da aka fi sani da Alhaji Sulaiman Bala.”
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Babban Editan kamfanin Mal. Ibrahim Musa ya sanya wa hannu a yau Talata.
Sanarwar ta kara da cewa, “Muna kuma isar da wannan ta’aziyyar ga Editan jaridar Almizan, Mal. Aliyu Saleh, wanda yake suruki ga marigayin.
“Har ila yau muna isar da wannan ta’aziyyar ga Shaikh Alhasan Sulaiman Bala, Sakataren ofishin Shaikh Zakzaky da sauran ‘ya’yan marigayin, musamman Shaikh Abdulmalik Sulaiman Bala, wanda yake ɗalibta a jamhuriyar Musulunci ta Iran,” a cewar takardar sanarwar.
Haƙiƙa jaridar ALMIZAN ta ci gajiyar sana’ar marigayin ta sayar da jaridu a birnin Kaduna tun kafuwarta kimanin shekaru 35 da suka shuɗe. Kuma ko da ya yi ritaya daga sana’ar, bai gushe ba yana sayen jaridar yana kai wa manyan mutane suna karanta ta, wanda hakan ya sa jaridar ta shiga lunguna da saƙunan da mutum ma bai yi zata ba.
Mai shekaru 75, Marigayi Alhaji Sulaiman Bala ya rasu ne a gidansa da ke Kaduna a ranar Lahadi, 5 ga Oktoba, 2025. Kuma ya bar ‘ya’ya 35, maza 20, mata 15. Tuni aka yi janazarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Aka binne shi a Maƙabatar Bashama Road da ke Tudun Wada, Kaduna.
Babban Editan ya ce, “Lalle mun yi rashin Uba, mai ba mu shawarwari da kuma tallafa mana a koyaushe.
“Allah ya gafarta masa kurakuransa, kuma ya ba shi Aljanna maɗaukakiya, amin,” in ji sanarwar.