Ba da yawu na Sa’idu Enagi ya yi rubutu kan siyasar Neja ba, kuma na dakatar da shi – Ministan Yaɗa Labarai

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa ba da yawun sa wani hadimin sa mai suna Sa’idu Enagi ya yi wani rubutu kan siyasar Jihar Neja ba.

Shi dai Enagi, ya wallafa sharhin ne a kafafen yaɗa labarai da taken “Malagi 2027”, inda ya yi wani hasashe kan wasu shirye-shirye da ya ce ana yi dangane da zaɓen gwamnan Jihar Neja na shekarar 2027.

Sai dai kuma Ministan ya barranta da rubutun gaba ɗaya tare da dukkan abin da ya ƙunsa.

A wata sanarwa da
Mataimaki na Musamman kan Kafafen Yaɗa Labarai ga Ministan, wato Rabi’u Ibrahim, ya bayar a ranar Laraba, ya ce Ministan ya duƙufa haiƙan kan aikin sa na gudanar da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta Tarayya, kuma ba shi da lokacin shagaltuwa da harkokin siyasa.

Ya ce: “Don haka, a yi watsi da wannan rubutun domin Mai Girma Ministan bai bayar da umurni ba kuma bai amince da wallafa shi ba.”

Ya ƙara da cewa Ministan ya bayar da umurnin yin bincike cikin gaggawa, kuma an bai wa Enagi takardar dakatarwa daga aiki ba tare da ɓata lokaci ba.

Ya ce: “Ya dace a lura da cewa Mai Girma Ministan da gwamnan jihar sa, Mai Girma Mohammed Umaru Bago, suna da kyakkyawar dangantaka ta fahimtar juna domin cigaban Jihar Neja gaba ɗaya. Saboda haka, duk wani hasashe game da zaɓen 2027 na iya kawo cikas ga waɗannan manufofi masu daraja.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *