Buba Marwa, Mutum Mai Baiwa Da Jajircewa Ya Cika Shekara 72
Daga Femi Babafemi
Na san Burgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya) kusan shekaru 30 da suka wuce. Lokacin ina matashin ɗan rahoto a gidan jarida, amma daga nesa na riƙa nazarin yadda a matsayin sa na gwamnan mulkin soja, Marwa ya bambanta da kowa, musamman dangane da irin jajircewar sa da kishin aiki ka-in-da-na’in har ya zama wani gwarzo kuma tauraron nuna ƙwarewar iya mulki. A wancan lokaci da gwamnatin sojoji kan nesanta daga jama’a farar hula, shi kuma Marwa sai ya zama hantsi leƙa gidan kowa, nagari na kowa a Jihar Legas, cibiyar da aka fi nuna adawa da mulkin soja.
Sai kuma na yi sa’a, bayan shekaru ashirin da biyar, na samu kaina ina aiki kai-tsaye a ƙarƙashin sa, a matsayin oga na. Tun daga wannan lokaci har yanzu, ya kasance babban ginshiƙin shugabanci da ƙwarin ƙwarin-guiwa. Lallai wasu mazajen gwarzaye ne: To Marwa na daga cikin irin waɗannan zaratan. Akwai labarai marasa iyaka dangane da kirki da mutuncin sa, hangen-nesa da abubuwan da ya cimma na rayuwa a aikace.
Duk inda ka karaɗe a duniya, daga birnin New York zuwa Washington; daga Barno zuwa Legas; daga Kaduna zuwa Abuja, har daga Legas zuwa Owerri – idan ka haɗu da wanda ya taɓa yin aiki tare da shi ko wanda ya san shi a matsayin shugaba a wurin aiki ko sanayya tsakanin mutum da mutum, zai riƙa baka labarai na alheri dangane da Marwa. Idan wani ya ƙara baka wani labarin dangane da shi kuma, za ka ƙaru da sanin wasu kyawawan halayen nasa daban-daban. Duk da sanin da na yi masa tsawon shekaru masu yawa, har yanzu ina jin wasu labarai na kyawawan halayen sa da ban taɓa ji a baya ba.
Yanzu da nake aiki a ƙarƙashin sa a Hukumar Hana Sha da Fataucin Muggan Ƙwayoyi (NDLEA) fiye da watanni 56, hakan ya ba ni damar bayyana irin halayen sa na ƙwarai, kuma na bayyana abin da ya bambanta shi da saura, ko dalilin da ya yi wa saura zarra, ya fita daban. A hakan, ni ma ina da labaran da zan bayar game da shi, dangane da batun aiki. Ba tare da shakku, tababa ko wani ɗar-ɗar ba, zan iya bugun ƙirji na ce: a duk inda ya yi aiki, wurin kan kasance ya samu sabon canjin yanayi, kuma zai bar gagarimin cigaba da za a riƙa tunawa ko cin-moriya shekaru masu dama masu zuwa, tsawon zamani, bayan ya bar wurin.
Daga cikin irin waɗannan labarai akwai matsayin da ya riƙe Mashawarcin Harkokin Tsaro a New York. Kafin hakan ya riƙe Mataimakin Mashawarcin Harkokin Tsaro a Ofishin Jakadancin Najeriya a Washington, kafin a maido shi gida Najeriya. Komawar sa ta biyu Amurka ce aka naɗa shi Mashawarcin Harkokin Tsaro a Ofishin Wakilin Najeriya na Dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya (UN). Irin gudummawar da ya bayar a lokacin kuwa har yau ana alfahari da shi.
Ta hanyar ƙoƙarin da ya yi ne har ya yi ƙoƙari ya samar wa dukkan waɗanda suka gaje shi a muƙamin gidan zama na dindindin. Wannan kuwa wata alfarma ce wadda a baya wani Mashawarcin Harkokin Tsaro a Ofishin Jakadancin Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya bai taɓa samu baya ba.
Kafin shi, bar waɗanda suka riƙe muƙamin kowa ya nemi gidan zama da kansa. Amma shi kuwa sai ya fahimci cewa ya dace a ɗauki nauyin samar wa duk mai riƙe da muƙamin gidan zama, sannan ya ya jajirce domin ganin hakan ya tabbata. A yau wannan babbar nasara da ya samar a ofishin ba za a taɓa mantawa da ita ba.
Irin wannan ƙoƙarin samar da gidan zama da Marwa ya yi a Washington, ya maimaita shi nan a Hukumar NDLEA, inda ya gina rukunin gidajen kwana, wato bariki-bariki ga jami’an NDLEA, abin da hukumar ba ta taɓa yi tsawon shekaru 35 bayan kafa ta ba. To haka Mohammed Buba Marwa yake. Duk inda ya yi aiki, sai ya kafa tarihin da ba ya kankaruwa. A DICON ma ya samar da gagarimin canjin da a baya ba a taɓa samar da kamar sa ba.
A Legas, ayyukan raya jiha da ya aiwatar masu yawa ne, waɗanda idan ana lissafa su, sai a riƙa kwatanta shi da gwarzon da ya ciwo gasas duniya ta wasannin Olamfik. Mazauna Legas a kullum suna tuna muhimman ayyukan cigaba da ya samar, suna santin nasarorin da ya samar masu. Shi ne ya fara samar da babura masu ƙafa uku, wanda a Legas aka raɗa wa suna ‘Keke Marwa,’ yanzu ga su nan birjik kowane gari a faɗin ƙasar nan. Wannan wata nasara ce ya samar wajen sauƙaƙe zirga-zirga a kan ababen hawa a Legas.
Sai kuma ɓangaren samar da kyakkyawan tsaro a cikin Legas ta hanyar kafa zaratan ‘Opetation Sweep; Operation 250 Roads, inda ya gina titina 250, gina rukunin gidaje masu yawa; Kwalejin Binciken Magunguna ta Jami’ar Legas da wurin yawon buɗe ido da shaƙatawa na Eko Tourist Beach Resort. Dukkan su kaɗan ne daga ayyukan raya jiha na tarihin Jihar Legas.
Al’ummar Jihar Barno sun daɗe da shaida irin ayyukan cigaban da Marwa ke sanarwa a duk inda ya yi aiki. Ya riƙe tsohuwar Jihar Barno lokacin da take haɗe da Yobe. Shi ya kafa Ma’aikatar Samar da Albarkatun Ruwa a jihar, kuma irin ta ta farko a Najeriya.
Yanzu da yake shugabancin NDLEA, a tsawon shekaru huɗu da rabin da ya yi, ya samar da gagarimin ci gaba. Hangen nesan sa da kyakkyawan jagorancin ya farfaɗo da wannan ƙasaitacciyar hukuma, ta hanyar bijiro da sauye-sauye na amfanin yanzu da ma na cin-moriya nan gaba. A yau ayyukan NDLEA ba a cikin Najeriya kaɗai suke yin tasiri ba, har ma a cikin ƙasashe maƙwabta da sauran ƙasashen duniya. Shi dai Marwa gani yake yi ba wani laƙanin iya aiki yake amfani da shi ba, abin a jinin sa yake. Amma dai ko da a jinin ne yake, to samun irin sa sai an tona.
A ƙarshe, kamar yadda nake yawan faɗa cewa Marwa mutum ne na daban a cikin mutane, wanda Allah ya ba baiwa da nasibin inganta rayuwar al’umma, saisaita akalar hukumomin gwamnati, ya kafa babban tarihi a kundin littatafan ayyukan inganta al’umma.
Yayin da yake cika shekaru 72 a duniya, a yau 9 ga Satumba, ina farin cikin bin sahun ɗimbin mutanen da ke masa fatan alheri, ƙara lafiya da cin nasarori a tsawon shekarun sa a duniya. Marwa jarumi ne abin tinƙaho: ya samu lambobin girmamawa na CON da OFR, ya samu sarautun gargajiya a yankuna daban-daban na Najeriya. Yana da digirin girmamawa har guda huɗu. Saboda haka taya shi murnar da muke yi, muna yi ne bisa cancanta da yi, kasancewar mun shaida sadaukarwar da ya yi wajen inganta rayuwar al’umma, hukumomi da cibiyoyi a faɗin ƙasar nan.
. Femi Babafemi shi ne Daraktan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai,
NDLEA, Abuja