Tsaro: Gwamnatin Tarayya Ta Ƙara Tura Sojoji a Jihar Zamfara Don Yaƙi da ‘Yan Ta’adda
Gwamnatin Tarayya ta kara tura karin sojoji zuwa jihar Zamfara domin ci gaba da yaki da ‘yan bindiga da sauran masu laifi a jihar. Ƙaramin Ministan Tsaro, Alhaji Bello Matawalle, ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar APC a Gusau a ranar Juma’a. “Ina nan tafe don haduwa da sojoji…
