Ashafa Murnai Barkiya
Bayanai daga Babban Bankin Najeriya (CBN) sun tabbatar da cewa an ƙara adadin kuɗin da za a iya cira ta hanyar amfani da katin ATM zuwa Naira dubu 100 a kowace rana.
Sabuwar dokar ta ƙara adadin kuɗin da za a iya cira daga dukkan hanyoyin biyan kuɗi zuwa N500,000 a kowane mako ga mutum ɗaya, daga asusun kuɗi ɗaya sai kuma adadin Nairs miliyan 5 idan kamfani ne.
A cikin wata sanarwa da CBN ya fitar a ranar Laraba, an bijiro da ƙarin cire kuɗi ta hanyar ATM zuwa N100,000 a rana, tare da adadin Naira 500,000 da sati ɗaya.
Wannan sabon tsari dai wani sauƙi ne idan aka kwatanta da takunkumin taƙaita cire kuɗi da aka kafa a gwamnatin da ta gabata.
A watan Disamba ne dai cikin 2022, lokacin tsohon gwamnan CBN Godwin Emefiele ya taƙaita cire Naira 100,000 kacal a mako da ATM ɗaya. Sai kuma Naira 500,000.
A yanzu CBN ya cire ƙa’idar adadin kuɗin ajiya a rana gaba ɗaya, yana cewa ba za a sake cajin kuɗin da suka wuce adadin ƙa’idar ajiya ba.
A cewar bankin, waɗannan manufofi suna daga cikin ƙoƙarin rage tsadar hadahadar kuɗi, inganta tsaro da kuma rage yawan karkatar da kuɗaɗe.
CBN ya bayyana cewa an samar da waɗannan manufofi ne tsawon shekaru don rage amfani da kuɗin hannu da kuma ƙarfafa amfani da hanyoyin biyan kuɗi na zamani.
Amma yanzu, bisa la’akari da “canjin lokaci”, an ga buƙatar daidaita dokokin domin su dace da halin da ake ciki a yanzu.
Sabbin dokoki za su fara aiki daga 1 ga Janairu, 2026, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Sai dai kuma za a ɗora kashi 3% kan adadin kuɗin da aka cira idan suka wuce waɗannan adadi. Yayin da su kuma kamfanoni za a caje su kashi 5% idan adadin kuɗin da za su cira ya wuce yadda aka gindaya.
An kuma umarci bankuna su riƙa miƙa rahotannin wata-wata da suka shafi cire kuɗin da suka wuce iyaka.
Haka kuma za su raba asusun da ake ajiyar kuɗaɗen cajin cire kuɗi da suka wuce adadi
Asusun da waɗannan dokoki ba su shafe su ba, sun haɗa da
asusun tara kuɗaɗen gwamnatin taarayya, jiha da. ƙaramar hukuma
Sai kuma asusun ‘microfinance’ da na bankunan bada lamuni ta hanyar jingina, wato ‘mortgage banks’.
Haka kuma wannan ƙa’ida ba ta shafi ofisoshin jakadanci, hukumomin diflomasiyya da kuma ƙungiyoyin bayar da tallafi na duniya ba.
