Shahararren malamin nan mai yawon jawo cece-kuce, Dk. Idris Abdul’aziz, ya rasu bayan fama da rashin lafiyar da ba a bayyana ba a jiya Alhamis 3 ga Afrilu, 2025 da dare.
Shafin sada zumunta na Facebook na masallacin sa, Dutsen Tanshi Majlis Bauchi, ya tabbatar da rasuwarsa, inda ya sanar da cewa za a yi jana’izar sa a filin Idi na Games Village da ke Bauchi da karfe 10:00 na safiyar yau Juma’a.
A cikin wasiyyarsa, Marigayin ya haramta daukar hoto a wajen jana’izarsa, ya soke taron tunawa da shi a gidansa, ya kuma hana mutane yin gogoriyin taba gawarsa da kuma shiga makabartar da takalmi.
Marigayin ya sha fama da cece-kuce da dama da kuma rashin jituwa da gwamnatocin baya a jihar Bauchi, sarakunan gargajiya, ‘yan sanda, ’yan uwa ’yan Izala da malaman Darika.
Ya samu digirin-digirgir a fannin shari’ar Musulunci a jami’ar Musulunci ta Madina da kuma digiri na uku a fannin shari’a a kasar Sudan.
A cikin sakon ta’aziyyar tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Digital Isa Pantami ya yi addu’ar Allah ya jikansa da rahama a Jannatul Fiddausi.