Rundunar Juyin Juya Hali ta Iran (IRGC) ta ce a ranar Asabar, makaman rokanta sun bugi wurare 14 na soja masu muhimmanci a Isra’ila da daddare.
Janar Ali Mohammad Naeini, mai magana da yawun IRGC, ya bayyana cewa “sakamakon harin roka da aka kai a yankunan da aka mamaye a zagaye na 18, an samu nasarar kai hari kan wurare 14 na soja masu muhimmanci a Haifa da Tel Aviv.”
Ya kara da cewa “ginin Sail Tower a tsakiyar Haifa, inda ofishin kamfanin AI12 Labs da wasu kamfanonin fasahar soji da ke karkashin ma’aikatar tsaron Isra’ila, an kai masa hari da rokar Qadr F mai dogon zango.”
Rundunar ta kara da cewa, “A daren nan, a zagaye na 19, an tura jiragen yaki da na kai farmaki masu yawa zuwa manyan wuraren soja daga arewa zuwa kudu na yankunan da aka mamaye.”
Rikicin ya fara ne 13 ga Yuni lokacin da Isra’ila ta kai hare-hare a wurare daban-daban a Iran, ciki har da sansanonin soja da na nukiliya, lamarin da ya sa Tehran ta mayar da martani da hare-haren roka.