Alhaji Abbas Sanusi, Galadiman Kano wanda ake matukar girmamawa, mai shekaru 91, ya rasu a ranar Talata biyo bayan doguwar jinya.
Kamar yadda PM News ta ruwaito, Abbas Sanusi sananne ne a masarautar Kano, inda ya taba kasancewa Wamban Kano kuma babban mai bayar da shawara a karkashin marigayi sarkin Kano Alhaji Ado Bayero daga shekarar 1963 zuwa 2020.
Shugaban jam’iyyar APC a jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya tabbatar da rasuwarsa a cikin wata tattaunawa ta wayar tarho a ranar Talata.
“Hakane, Baba ya rasu bayan doguwar jinya.
“A matsayinsa na daya daga cikin sanannu a masarauta, rasuwar Sanusi na nuni da wani babban rashi ga al’umma.” Kamar yadda ya bayyana.
Sanusi na da mataye da ‘ya’ya 35 ciki har da shugaban jam’iyyar APC a jihar Kano kuma za a yi jana’izarsa ne da karfe 9 na safiyar ranar Laraba a Fada.