Gobe Juma’a Za A Yi Jana’izar Sheikh Dahiru Usman Bauchi

An sanar da cewa an sa ranar gobe Juma’a domin yin jana’izar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamba a gidansa da ke Kofar Gombe a cikin garin Bauchi.

Hadiminsa M Daha Azhary Bauchi shi ne ya sanar da cewa za a yi jana’izar ne a ranar Juma’a

Ya ce, “Za a yi Sallar Jana’izar Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi a gobe Juma’a 28-11-2025 a Bauchi.”

Fitaccen Malamin wanda ya yi fama da jinya ya kasance wanda ya bayar da gudummawa sosai wajen ci gaban addinin Musulunci a Nijeriya da ma Afrika.

An haifi Sheikh Dahiru Usman ne a ranar 2 ga Almuharram 1346 A.H a garin Nafada da ke jihar Bauchi a wancan lokacin (yanzu tana jihar Gombe).

Sheikh Dahiru ya fara Tasirin Alkur’ani ne a Bauchi tun 1948. Ya kasance mai gudanar da tafsirin watan Ramadana a jihohin Bauchi da Kaduna.

Kafin rasuwarsa shi ne mataimakin shugaban kwamitin Fatwa na Majalisar koli ta addinin Musulunci (Supreme Council of Islamic Affairs.)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *