Hukumomin Najeriya sun tabbatar da kuɓutar da dalibai mata 24 na makarantar sakandire da ke garin Maga, Jihar Kebbi, waɗanda ‘yan bindiga suka sace a makon da ya gabata.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya sanyawa hannu, ta ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi farinciki da dawowar daliban, tare da jinjinawa jami’an tsaro bisa rawar da suka taka.
A wani bidiyo da aka wallafa bayan kuɓutar da su, an ga daliban a cikin wata babbar motar bas tare da jami’an tsaro, suna faɗin sunayensu ɗaya bayan ɗaya. Bidiyon ya kuma nuna su cikin murna da annashuwa yayin da ake tafiya da su zuwa sada su da iyalan su.
Shugaba Tinubu ya yi kira ga jami’an tsaro da su ƙara ƙaimi wajen kokarin ceto sauran daliban Jihar Neja da har yanzu ke hannun ‘yan bindiga.
Tun bayan sace daliban ne gwamantin tarayya ta ɗauki matakai daban-daban domin ganin an sako su, ciki har da aikewa da ƙaramin ministan tsaro, Mohammed Bello Matawalle, zuwa Kebbi domin sa ido a kan aikin ceto ɗaliban.
