Jagoran juyin-juya-halin Musulunci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya ce “Isra’ila ta shirya shan uƙuba” bayan hare-haren da ta ƙaddamar cikin dare kan cibiyoyin nukiliya na Iran da kuma kashe manyan jami’an sojinta.
Ya ce Isra’ila “ta aikata mummunan laifi a cikin ƙasarmu a yau” kuma dakarunsa “ba za su taɓa bari lamarin ya tafi haka nan kawai ba”.
“Kan wannan laifi, Isra’ila ta tsoma kanta cikin mummunar makoma, kuma za ta girbi abin da ta shuka.”
Rundunar sojin Isra’ila ta IDF ta ce tuni Iran ta kai mata farmaki da jirage marasa matuƙa sama da 100.
Sai dai ƙasashen Larabawa da ke tsakanin Iran da Isra’ila da kuma Amurk da Birtaniya tuni sun umurci dakarunsu su kakkabo jiragen tun kafin su isa Isra’ilan.
Shi ya sa masharhanta ke ganin jirage marasa matuka kadan ne cikin waɗanda Iran ta aika za su iya isa Isra’ila.
Amma kuma wannan ana ganin martanin Iran ne na gaggawa, sahihin martanin na nan tafe kamar yadda Jagora ya alkawarta.