Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya zai yi zaman gaggawa kan yankunan Falasdinawa

Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya zai yi zaman gaggawa a yammacin ranar Alhamis domin tattaunawa kan halin da ake ciki a Gaza da kuma Yamma da gabar kogin Jordan biyo bayan bukatar hakan daga kasar Aljeriya.

Kamar yadda kafar watsa labaru ta The New Arab ta ruwaito, kiran na kasar Aljeriya na zuwa ne biyo bayan karuwar hare-haren Isra’ila a zirin Gaza tare da kuma rashin kwanciyar hankali a Yamma da gabar kogin Jordan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *