A ƙarshen makon nan ne, makarantar Salmanul Farisi da ke Hayin Ɗanmani Kaduna, ta yi bikin yaye ɗalibai 96 da suka haddace Alƙur’ani mai tsarki, ’yan diploma da kuma waɗanda suka yi sauka.
Taron, wanda ya gudana a harabar makarantar, ya samu halartar ɗimbin jama’a maza da mata, ciki har da Wakilin Jami’atul Mustafa a Nijeriya, Hujjatul Islam wal Muslimin Dakta Mustapha Ƙayediyan, wanda Dakta Shu’aibu Muhammad Shugaban makarantar Khatamul Anbiya ya wakilta.

A jawabinsa a taron, Shaikh Shu’aibu Muhammad, ya jawo hankalin iyaye a kan muhimmanci kula ga ’ya’yansu da suka samu baiwar haddace Alƙur’ani domin sun samu alheri mai yawa. “Ina kira ga iyaye, inda Allah ya ba ka ɗa mai karanta Alƙur’ani a gidanka, ka sani fa Allah ya yi maka alheri mai yawa. Ka san kimar wannan ɗan naka da yake karanta Alƙur’ani a gidanka.
“Riwaya tana nuna cewa gidan da ake karanta Alƙur’ani, Mala’iku suna kallon haskensa daga sama kamar yadda ake kallon tauraro daga ƙasa. A lokacin da ake ganin taurari wannan na haske a nan, wannan na haske a nan, gidajen da ake karanta Alƙur’ani, haka Mala’iku suke kallon su. Ga gidan wane can yana haske. Ka ga ɗan da ya zama sanadin haske a gidanka, wanda har Mala’iku za su shaida gidanka saboda karatun ɗanka, ya kamata ka san kimar wannan yaron, ka tsaya ka yi masa tarbiyyar da ta dace domin ya kasance mai amfanarwa.”
Shaikh Shu’aibu Muhammad, wanda ya yi nuni da irin alherin da ke ƙunshe cikin yi wa al’umma hidima, ya bayyana cewa; “Irin wannan hidima da ake yi wa al’umma, ba wani alherin ya kai shi. A ce a gina al’umma a kan ilimi, kuma ilimin ɓangare guda biyu, -na duniya da kuma na addini-, musamman a ɗora al’umma kan Alƙur’ani. Wannan ba ƙaramin abu ne mai kima da daraja ba.
“Idan muka kalli wannan taron tun daga safe zuwa lokacin da na riske shi zuwa yanzu, za ka ga mafi yawan abubuwan da ake yi shi ne Alƙur’ani, kuma da ma Allah ya faɗa cewa Alƙur’ani shi ne ke kiran mutane zuwa ga shirya. Shi ne wanda yake shiryar da al’umma hanya madaidaiciya.
“Shi ya sa ma Manzon Allah (S) ya haɗa su abu uku, ya ce ‘ku ladabtar da ’ya’yanku a kan abubuwa guda uku, son Annabinku, da son iyalansa da karatun Alƙur’ani.’ Muna da tabbacin al’ummar da suka taru a kan matakin farko masoya Manzon Allah ne, mataki na biyu masoya Ahlul Baiti ne, sannan kan Alƙur’ani ba sai mun tambaya ba.”
Da yake tsokaci kan muhimmancin sanar da matasa Alƙur’ani da kuma ma’anoninsa, Dakta Shu’aibu Muhammad ya tabbatar da cewa; “Duk lokacin da aka cika zukatan matasa da Alƙur’ani, an cika ta da alherin duniya da lahira, musamman in ya zama bayan Alƙur’anin ana ƙoƙarin sanar da su ma’anonin Alƙur’ani ɗin.”
Ya jadadda cewa saɓani da rashin fahimtar da ake samu a tsakanin al’ummar Musulmi ya biyo bayan rashin fuskantar da zuciya zuwa ga Alƙur’ani ne. “A wannan duniyar da muke ciki, wannan saɓanin da ake samu da gaske akwai ƙarancin tawajjuhi zuwa ga Alƙur’ani da buɗaɗɗiyar zuciya. Idan aka kalli Alƙur’ani da buɗaɗɗiyar zuciya ba a rufe ba, abin da nake nufi da buɗaɗɗiyar zuciya shi ne, kar ya zama ka sa Alƙur’anin kana son ya tafi tare da ra’ayinka, ina son Alƙur’ani ya haska min hanya. Shi ya sa za ka ji Allah yana cewa ‘ka yi bushara ga bayina, sune waɗanda suke sauraron magana su bi mafi kyaunta. Idan mutum ya samu tarbiyya ta Alƙur’ani da sanin ma’anar Alƙur’ani, zai wahala ka ji ana rigima da shi. Duk inda ya ji wani abu zai ga cewa me ya dace da Alƙur’ani? Sai ya riƙe. Me ya dace da koyarwar Manzon Allah (S)? Sai ya riƙe.”
A ƙarshe Shaikh Shu’aibu Muhammad ya taya ɗaliban da suka haddace Alƙur’ani da waɗanda suka kammala karatunsu a matakin diploma da sauran waɗanda suka yi sauka murnar wannan babbar nasarar da suka samu a rayuwa. “Muna taya su murna, Allah Maɗaukakin Sarki ya albarkaci rayuwarsu.”
Shaikh Sha’aibu Muhammad dai ya jagoranci tawagar makarantar Khatamul Anbiya da ke Kano zuwa wajen taron ne, sannan kuma ya wakilci Wakilin Jami’atul Almustafa a Nijeriya, Dk. Mustapha Ƙayediyan. Ya ce, “Na wakilici tawagar makarantar Khatamul Anbiya da ke Kano, sannan kuma da wakilci na Jami’atul Mustafa.”

A jawabansu daban-daban Dakta Ibrahim Al-azhari Annajafi da Sidi Muhammad Bello Al-Bashir Al-Jazari sun jawo hankalin iyayen yara a kan muhimmancin kula da ilimin ’ya’yansu, tare da bayyana irin tagomashin da ke ƙunshe cikin ƙarfafa gwiwar yara wajen samun ilimin Alƙur’ani.
Kafin a tashi taron, sai da ɗaliban makarantar suka karrama Shaikh Hashimu Badiko da lambar girmamawa, saboda nuna farin ciki da irin namijin ƙoƙarin da yake yi dare da rana don ya kyautata rayuwarsa da ɗora su a kan gwadaben ilimi da tarbiyya.
Shi kuwa Dakta Mustapha Ƙayediyan ya aiko da kyautar Naira dubu 20 ga ɗaliban da suka yi sauka yi, kamar yadda Shaikh Shu’aibu Muhammad ya sanar, yayin da haramin Abul Fadal Abbas ya aiko da takardar shaida ga ɗaliban da aka yaye.

Taron ya samu halartar manyan baƙi daga ciki da wajen garin Kaduna, ciki har da Wakilin ’yan’uwa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzkay (H); Malam Aliyu Tirmidhi, Sarkin Hayin [anmani Alhaji Abba, O.C. na ’yan sanda (outpost na Ɗanmani), babban Editan jaridar ALMIZAN; Malam Ibrahim Musa, Malam Ahmad Rufa’i (Sarkin Kinkinau), mataimakin Shugaban ƙungiyar Ahlul Baiti Political Forum; Alhaji Usman Abubakar, Shugaban Ahlul Bait Political Forum reshen Kaduna; Alhaji Isah Muhammad da Malam Abubakar Bazanga; Shugaban Bazanga Foundation.
