Ministan Labarai Ya Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Tsohon Shugaban Ƙasa

A safiyar yau, Laraba, Ministan Labarai, Alhaji Mohammad Idris Malagi, ya kai ziyara ta ta’aziyya ga tsohon shugaban ƙasa, Abdulsalami Abubakar, a garin Minna, babban birnin Jihar Neja.

A yayin ziyarar, Ministan ya halarci Addu’ar Fiddau a gidan Marigayya Hajiya Talatu, ƙanwarsa tsohon shugaban ƙasa, sannan ya ziyarci gidan Marigayi Ambasada Manta, wanda ya rasu kwanan nan.

Ana roƙon Allah ya yi wa marigayin gafara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *