Shugaban Karamar Hukumar Katagum Ya Raba Kayan Tallafi Don Dogaro Da Kai

Daga Idris Ibrahim Azare

13/5/2025 shugaban ƙaramar hukumar katagum, Hon. Yusuf Babayo Zaki ya ƙaddamar da shirin rabon tallafi na kayan Sana’a, noma, mota da kuma babura ga al’umar mazabar sa.

Rabon wanda irin sa ya kasance na farko a shugaban cin ƙaramar hukumar Katagum Hon. Yusuf ya bada sabin babura roba roba ga dukkan kansiloli 20 da suke a ƙaramar hukumar tare da S.A Community guda 1 da kuma ƙarin mutane 6

Kyautar da ya ayyana a matsayin kyautata wa don saukaka zuwa wajen aiki akan lokaci da kuma zirga-zirgar jama’a, haka zalika ya bayar da kekunan saƙa, injin ban ruwa, injin markade, injin Nika, injin murza taliya ga mata da matasa don dogaro da kansu., da kuma wayoyin hanu ga  ‘Yan media domin karfafa masu aikinsu.

A ɓangaren kiwon lafiya ya samar da kayayyakin gwaje-gwaje, katifu da gadajen kwantar da marasa lafiya a asibiti, littafai da abin karatu don taimakon ɗalibai na matakin karatun farko a makarantun faramare na ƙaramar hukumar Katagum.

Sannan ya bayar da kyautar mota ga shugaban jam’iyar PDP na ƙaramar hukumar Katagum Mercedes-Benz shima don kyautata wa tare da rabon tsabar kuɗi ga mutane da dama masu ƙananun sana’a domin dogaro dakai

Har ilau lokacin da yake ƙaddamar da shirin ya sanar da ɗaukan ma’aikata a fannoni dabam-dabam wanda za’a rinka biyan su a ƙaramar hukumar Katagum. 

Taron wanda aka yi a farfajiyar sakateriyar ƙaramar hukumar ya sami halartan mataimakin shugaban jam’iyar PDP na jihar Bauchi, Alh. Falalu Attah, shugaban jam’iyar PDP na ƙaramar hukumar katagum Hon. Kabiru Halilu, shugabannin ƙananan hukumomin Giade, Darazo, hakimai da dagatai na ƙasar katagum.

Mutanan da suka sami wadannan kyautuka sun nuna farin cikinsU da wannan kaya da aka basu WaNda za su dogara da kansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *