Rundunar sojin Najeriya ta samu gagarumar nasara a yakin da take da ta’addanci a jihar Zamfara, bayan da dakarun Mobile Strike Team (MST) na Operation FASAN YAMMA (OPFY) suka hallaka wasu fitattun ‘yan ta’adda a cikin wani sumame da suka kai a yankin Ƙunchin Kalgo, karamar hukumar Tsafe, ranar Litinin 10 ga Yuni, 2025.
Cikin wadanda aka kashe har da shahararren shugaban ‘yan ta’adda da aka fi sani da AUTA, tare da abokan aikinsa Abdul Jamilu da Salisu, wadanda suka dade suna sanya fargaba da tashe-tashen hankula a yankin.
Wasu manyan shugabannin yan bindiga guda biyu, ciki har da wanda aka tabbatar da sunansa da Babayé sun hallaka a yayin artabun. Hakazalika, dakarun soji sun kashe Sale Ado Madele (wanda ake kira Sarki), ɗa na fari ga shahararren ɗan bindiga, Ado Alieru a wani harin na daban a Zamfara.
Dakarun Operation Fasan Yamma, sun kuma hallaka wasu karin ’yan ta’adda goma da suka taru a kusa da wata tashar mai da ke garin Danjibga, wadanda ake zargin suna shirin kai hari bisa jagorancin wani da aka fi sani da Dogo Sule.
Wannan samame ya zama babban koma baya ga ‘yan ta’adda da ke yunkurin hana zaman lafiya a Zamfara da wasu sassa na Arewa maso Yamma. Rundunar sojin Najeriya ta sake jaddada aniyarta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.