Sojojin Najeriya sun kashe mataimakin kwamandan ’yan bindiga a Jihar Kogi

Sojojin Najeriya na Runduna ta 12 da ke Lokoja sun tabbatar da kashe wani fitaccen mataimakin kwamandan ’yan bindiga a Jihar Kogi, Babangida Kachala.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Laftanar Hassan Abdullahi, ya fitar ta ce an samu nasarar ne a ranar 11 ga Satumba, ƙarƙashin Operation Accord III, tare da haɗin guiwar rundunonin tsaro na haɗaka (OHF).

Abdullahi ya ce rundunar ta samu sahihin bayani kan motsin ’yan bindiga a dajin Ofere da yankin Ayetoro Gbede a ƙaramar hukumar Ijumu, inda suka shirya musu tarko.

An yi musayar wuta mai zafi, inda sojojin suka yi nasarar hallaka ɗaya daga cikin manyan kwamandojin.

Sojojin sun gano kaya da dama a wajen harin, ciki har da Magazine mai ɗauke da harsasai, wayoyin hannu guda 31, magunguna irin su Tramadol, kayan tsafi, na’urar auna hawan jini, da kuma kuɗi naira 16,000.

Haka kuma, an ga jini a wajen, abin da ke nuna cewa wasu daga cikin ’yan bindigar sun tsere da raunukan harbin bindiga.

Bayan bincike daga baya ya tabbatar cewa Babangida Kachala, wanda shi ne mataimakin shugaban ƙungiyar yan bindiga ta Kogi, Kachala Bala Shuaibu, shi ma ya mutu daga raunukan da ya samu.

Rundunar sojojin ta tabbatar wa jama’ar Najeriya ƙudirin ta na kawo karshen ayyukan ’yan bindiga da tabbatar da zaman lafiya.

Haka kuma ta yi kira ga al’umma da su ci gaba da bayar da ingantattun bayanai domin taimakawa a nasarar ayyukan tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *