Ta’aziyya: Dan Agbese gwarzo ne na haƙiƙa a fagen aikin jarida, inji Ministan Yaɗa Labarai


Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana alhini kan rasuwar fitaccen ɗan jaridar nan, Cif Dan Agbese, wanda ya rasu a ranar Litinin.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Abuja, Idris ya ce: “Na yi matuƙar baƙin ciki da mutuwar Mista Dan Agbese, ginshiƙi a aikin jarida na zamani a Nijeriya kuma mai jajircewa wajen kare ‘yancin aikin jarida.”

Ya bayyana marigayin a matsayin “gwarzon kare gaskiya wanda aikin sa ya kafa tushen tattaunawar jama’a ta wayewa ta hanyar kasancewar sa ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa mujallar Newswatch, wadda ta zama babbar cibiya a rayuwar mu ta ƙasa.”

Ya ƙara da cewa: “Haƙiƙa, ya tsaya tsayin daka wajen kare ƙimar jarumta, gaskiya ta hankali, da kuma jajircewa marar yankewa wajen kare ‘yancin ‘yan jarida, waɗanda su ne ainihin ginshiƙan dimokiraɗiyya mai ƙarfi.”

Ya tuna da cewa ta hanyar shafin sa na “No Holds Barred” da kuma aikin da ya yi a tsawon rayuwar sa, Agbese ya sa masu mulki sun yi bayani, kuma ya sadaukar da rayuwar sa ga aikin gina ƙasa.

Ministan ya ce rasuwar Agbese ta faru ne a daidai lokacin da Gwamnatin Tinubu take ƙara himma wajen inganta abubuwan da marigayin ya tsaya kai-da-fata a kan su – wato faɗaɗa sararin dimokiraɗiyya, ƙarfafa shiga cikin harkokin ƙasa, da kare ‘yancin faɗar albarkacin baki.

Ya ce: “Don haka, ina alhinin rasuwar sa ba kawai da baƙin ciki ba, amma da godiya mai zurfi ga wani gado wanda ya yi tasiri a kan tattaunawar ƙasar mu.”

Ya ƙara da cewa, “Ina miƙa saƙon ta’aziyya ta ga iyalin sa, abokan aikin sa da dukkan ‘yan’uwa a fagen aikin jarida.”

A cewar Idris, “Dan Agbese babban ginshiƙi ne, kuma gudunmawar da ya bayar za ta ci gaba da haskaka wa Nijeriya hanya. Allah ya jiƙan sa da rahama.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *