ZAFAFAN RADDIN ABBA GIDA-GIDA GA GANDUJE: ‘Ba ka da kunya har ka ke borin-kunyar shekara takwas da ka yi ka na tafka gadangarƙama a Kano’
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir-Yusuf, ya maida wa tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje zafafan raddi, dangane da zargin kasawar da ya ce gwamnatin Kano ta yanzu ta yi a watannin goma da ta yi ta na mulki. PREMIUM TIMES Hausa ta ruwaito Gwamna Abba ya ce shekaru takwas na mulkin Ganduje cike suke maƙil da…
