TALLAFIN GWAMNATIN TARAYYA: Kano za ta raba ƙaramin buhun shinkafa lodin mota 100, buhun dawa lodin mota 44, buhun gero lodin mota 14, buhun masara lodin 41 a faɗin jihar
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa za ta yi rabon tallafin kayan abincin da Gwamnatin Tarayya ta ba jihar. Cikin sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya yi wa taron manema labarai a ranar yammacin Lahadi, ya ce Jihar Kano ta karɓi lodin mota 100 na ƙaramin buhun shinkafa, na…
