Ministan Yaɗa Labarai da Darakta Janar na VON sun yi alhinin rasuwar babbar ‘yar jarida Rafat Salami
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya jajanta wa iyalan Hajiya Rafat Salami, babbar ‘yar jarida a gidan rediyon Muryar Nijeriya (VON) kuma Ma’ajin Cibiyar Yaɗa Labarai ta Duniya (IPI), wadda ta rasu a ranar Juma’a a Abuja. Da yake bayyana rasuwar tata a matsayin “babban rashi ba kawai ga iyalan…
