BAN CE NA GOYI BAYAN ƘUDIRIN GYARAN DOKAR HARAJI ƊARI BISA ƊARI BA: INA BADA HAKURI NA RASHIN FAHIMTA -Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa
Ina jan hankalin al’ummar ƙananan hukumomin Ƙiru da Bebeji, Jihar Kano, Arewa da Nigeria cewa BABU WURIN DA KO SAU ƊAYA NA CE INA GOYON BAYAN SABABBIN DOKOKIN HARAJI ƊARI BISA ƊARI. Abin da nace, akwai batutuwa da dama waɗanda za su zama alheri ga Arewa da Nigeria. Kuma mu yan Majalisa na yankin arewa…
