Matsalar tsaron Nijeriya tana hana ni barci, inji Tinubu a taron cikar ACF shekaru 25
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce babu wata babbar damuwa da ke tasiri a zuciyar sa fiye da matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara a Nijeriya, musamman tashin hankalin da ya addabi sassa da dama a Arewa. Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Asabar a Kaduna, yayin bikin cikar Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa…
