Gwamna Dauda ya bayyana alhinin mutuwar Shugaban Bankin Access, Herbert Wigwe
Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana mutuwar Shugaban Bankin Acces, Herbert Wigwe, a matsayin babban rashi ga harkar banki a Nijeriya. Idan dai ba a manta ba, Herbert Wigwe ya mutu tare da matarsa da ɗansa a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a California kusa da kan iyakar Nevada da ke Ƙasar Amurka….
