Tinubu Ya Gwangwaje ‘Yan Super Falcons Da Kyautar Dala 100,000 Da Kuma Gida Kowannen Su
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karrama ‘yan rundunar ƙwallon ƙafa ta mata ta Nijeriya, wato Super Falcons, da kyautar karramawa ta ƙasa da kuma kyautar kuɗi da ta gidan kwana saboda nasarar su a gasar Kofin Ƙasashen Afrika na Mata (WAFCON), wanda aka gama ranar Asabar, inda suka ciyo kofin a karo na 10….
