Gwamnan Zamfara zai inganta Asibitin Kwararru na Yariman Bakura
Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya amince da shirin gyara, tare da sake inganta asibitin ƙwararru na Yariman Bakura da ke Gusau domin magance ƙalubalen da ake fuskanta na samar da ingantacciyar kiwon lafiya a Jihar Zamfara. Gwamnan ya amince da aikin gyaran asibitin ƙwararrun ne a ranar Litinin a taron Majalisar Zartarwa karo na…
