Tinubu yana gina ginshiƙi mai ƙarfi na makomar Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce manufofi da shirye-shiryen gwamnatin Tinubu sun fara samar da ribar dimokiraɗiyya ga ‘yan ƙasa. Ya faɗi haka ne a safiyar yau yayin tattaunawa da ƙungiyoyin goyon bayan jam’iyya mai mulki, wato APC, a ofishin sa da ke Radio House, Abuja. Idris ya ce:…
