Gwamnati za ta sake zuba kuɗin da ake tarawa daga janye tallafin wutar lantarki wajen inganta wutar lantarki, kiwon lafiya, da ilimi, inji Ministan Yaɗa Labarai
Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce sama da naira tiriliyan 1 da za a tara daga janye tallafin wutar lantarki za a sake zuba su ne wajen inganta wutar lantarki, kiwon lafiya, da ilimi ga ‘yan Nijeriya. Da yake jawabi a matsayin babban baƙo na shahararren shirin Rediyo Nijeriya…
