Nijeriya Za Ta Gudanar da Taron Farko na IPI Afrika – Minista
Nijeriya ta amince da karɓar baƙuncin babban taron farko na ƙasashen nahiyar Afrika na Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Duniya (IPI). Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a wurin wani taro da aka gudanar a birnin Vienna na ƙasar Austriya, inda ya gana da Shugaban Kwamitin Zartarwa…
