Jami’ar NOUN za ta ba Hafsatu Abdulwaheed da Innocent Chukwuma digirin girmamawa, Za ta yaye ɗalibai 22,175
BUƊAƊƊIYAR Jami’ar Nijeriya (NOUN) za ta bayar da digirin girmamawa na dakta ga wasu hamshaƙan ‘yan Nijeriya biyu, wato Hajiya Hafsatu M.A. Abdulwaheed da Cif Innocent Chukwuma, a ranar Asabar mai zuwa. Mataimakin Shugaban jami’ar, Farfesa Olufemi A. Peters, shi ne ya bayyana haka a wajen taron manema labarai da ya yi a Abuja a…
