Gwamna Lawal Ya Gabatar da Kasafin Naira Biliyan 861 Ga Majalisar Dokokin Jihar Zamfara
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gabatar da ƙudirin kasafin kuɗi na shekarar 2026 mai darajar Naira Biliyan 861 ga Majalisar Dokokin Jihar, inda ya bayyana shi a matsayin taswirar sauyi da kuma shaida cewa Zamfara na kan hanyarta ta tashi tsaye da ƙarfi. An gabatar da kasafin ne a ranar Alhamis a birnin Gusau….
