Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan tsaro tare da ba da umarni ga jami’an tsaro da su ɗauki ƙarin ma’aikata

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan harkokin tsaro a fadin kasar, tare da bayar da umarnin daukar karin jami’an tsaro da zummar karfafa yaki da ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta. A cikin wata sanarwa daga fadar shugaban kasa da aka fitar ranar Laraba, Shugaba Tinubu…

Read More

Rundunar Sojin Najeriya Ta Ce Za Ta Cigaba da Tsananta Bincike Har Sai an Gano Duka Ɗaliban da aka sace a Makon da ya shuɗe

Rundunar Sojan Najeriya ta ce dakarunta na Operation Fansan Yamma na ƙara tsananta bincike domin gano daliban da aka sace a jihohin Neja, Kebbi da Zamfara. Majiyar tsaro daga Hedikwatar Soja ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) cewa dakarun sun yi nasarar halaka ‘yan ta’adda da kuma lalata sansanoninsu a sassa daban-daban…

Read More

Tawagar da Gwamnatin Tarayya ta tura zuwa Amurka tana samun nasarar magance labaran ƙarya game da yanayin tsaron Nijeriya, inji Ministan Yaɗa Labarai

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa tawagar manyan jami’an Gwamnatin Tarayya da ta tafi ƙasar Amurka a ƙarƙashin jagorancin Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro, Malam Nuhu Ribaɗu, tana gudanar da aiki sosai wajen magance labaran da ake yaɗawa na ƙarya da ke nuna wai ana…

Read More