Rasuwar Buhari: Gwamnatin Tarayya ta aika Shettima Landan domin jagorantar dawo da gawar marigayin Najeriya
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu yau da misalin ƙarfe 4:30 na yamma a birnin London, bayan fama da doguwar rashin lafiya. Shugaba Tinubu ya kuma miƙa ta’aziyya ga matar marigayin, Hajiya Aisha Buhari tare da mika sakon alhini da juyayi a madadin kansa…
