Fadar Shugaban Ƙasa Ta Karyata Jita-Jitar Hana Shettima Shiga Villa
Fadar Shugaban Ƙasa ta musanta jita-jitar da ke cewa an hana Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, shiga fadar shugaban ƙasa. A wata sanarwa da mai taimaka wa Shugaban Ƙasa kan harkokin watsa labarai a ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Stanley Nkwocha, ya fitar, ya bayyana cewa labarin karya ne marar tushe da nufin tada zaune tsaye…
