Mazauna Sokoto Sun Yi Murna Bayan Nasarar Kashe Fitattun ‘Yan Bindiga 3 A Jihar
Al’ummar kauyukan da ke Mallamawa da Mazau a yankin Tsamaye/Mai Lalle dake Ƙaramar Hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto, sun yi murna da farin ciki bayan nasarar da sojojin hadin gwiwa na ‘Operation FANSAN YAMMA (OPFY)’ suka yi na kashe manyan shugabannin ‘yan bindiga uku a yankin. A cewar jami’in watsa labarai na OPFY, Kyaftin…
