DA DUMI-DUMI: An sako Ɗaliban makaranta 130 da aka sace a Jihar Neja
An saki dukkan ɗaliban makaranta da aka sace daga makarantar St. Mary’s Catholic School da ke Papiri a Jihar Neja. An kubutar da rukunin ƙarshe mai ɗalibai 130, lamarin da ya kai adadin waɗanda aka ceto gaba ɗaya zuwa 230. Jami’an Ofishin Mai baiwa sugaban kasa shawara kan harkokin tsaron Ƙasa sun tabbatar da hakan…
