Rundunar Sojin Najeriya sun fatattaki gungun ‘yan bindiga a Shanono tare da kashe 19 daga cikin su
Sojojin rundunar hadin gwiwa ta Operation MESA a Jihar Kano sun yi nasarar dakile wani yunkurin hari da ‘yan bindiga suka kai a yankin Shanono, a yammacin ranar Asabar, 1 ga watan Nuwamba, 2025. A cewar sanarwar da rundunar ta 3 Brigade ta fitar, sojojin tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro sun samu bayanan…
