Yaƙi Da Cutar Kansa: Uwargidan Gwamnan Zamfara, Hajiya Huriyya Ta Zama Sakatariyar Ƙungiyar FLAC

Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda, ta zama Sakatariyar Gamayyar Ƙungiyar Matan Shugabannin Nijeriya Masu Fafutukar Yaƙi da Cutar Daji (FLAC). Ƙungiyar tana faɗi-tashi wajen yaƙi da cutar kansa ta ta hanyar wayar da kai, tsara manufofi da kuma shiga tsakani kai-tsaye ga al’umma. Naɗin nata ya nuna matuƙar jajircewa da irin gudunmawar da…

Read More

Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar da Shirin Ciyarwa A Makarantun Zamfara, Ya Ƙudiri Aniyar Magance Matsalar Yara Da Ba Sa Zuwa Makaranta

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatin sa na magance matsalar yawaitar yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar. Gwamnan ya ƙaddamar da shirin Ciyar da Ɗaliban Makaranta ta Jihar Zamfara ranar Alhamis a makarantar firamare ta Dan-turai da ke Gusau, babban birnin jihar. Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan…

Read More