TARON WAYAR DA KAI A ENUGU: ‘Doka ta bada damar hukunta masu wulaƙanta takardun Naira’ – CBN

Ashafa Murnai Barkiya

Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya yi kakkausan gargaɗi cewa dokar ƙasa ta tanadi hukunci kan masu wulaƙanta takardun Naira.

Gargaɗin ya fito ne daga bakin Daraktar Riƙo ta Sashen Hulɗa da Jama’a, Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Hakama Sidi Ali.

Ta yi wannan gargaɗi a wurin taron gangamin wayar da kai da CBN ya shirya, ranar Talata, a Enugu.

Ta ce duk wani nau’in wulaƙanta takardun Naira, akwai dokar da ta tanadi hukunci a kan sa. Saboda haka ta yi kira ga ‘yan Nijeriya su riƙe tare da tu’ammali da takardun Naira cikin daraja da tsafta.

“Lallai muna jaddada kira da babbar murya ga ‘yan Nijeriya cewa: su daina watsi da Naira ko liƙi a wurin bukukuwa, su daina sayar da takardun Naira, a guji duƙunƙune Naira, sa mata datti da kauce wa kuɗin jabu. Saboda darajar takardar Naira darajar ƙasar mu ce.”

Ta ce riƙe takardun Naira ana hadahada da su a cikin daraja da tsafta, abu ne mai muhimmanci wajen inganta harkokin kuɗaɗe na yau da kullum, kuma hakan na ƙarfafa tsarin saye da sayarwa tsakanin mai biyan kuɗi da mai sayarwa.

Hakama ta kuma shawarci jama’a su riƙa dagaro da hanyoyin da CBN ya tanadar domin samun sahihan bayanan da suka shafi CBN, musamman kan abin da ya shafi tsare-tsare, ƙa’idoji da sharuɗɗan da CBN ke gindayawa.

Ta ce tsare-tsaren inganta tattalin arziki irin su saisaita tsarin musayar kuɗaɗen waje zuba na bai-ɗaya, sa-ido wajen yin aiki filla ba tare da nuƙu-nuƙu ba, hakan ya ƙarfafa tsarin hada-hadar kuɗaɗe, ya bunƙasa asusun kuɗaɗen waje, kuma yana kan kankaro wa Naira darajar ta a kasuwar musayar kuɗaɗe.

Daraktar ta ƙara da cewa a ƙarƙashin Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, an ɗauki ƙwararan matakai ɗora tattalin arziki kan miƙaƙƙar hanya, cikin matakan da ta ce an ɗauka har da ƙarfafa jarin bankuna da sauran su.

A wurin taron dai an bai wa masu ruwa da tsaki da sauran jama’a damar yin tambayoyi, ana kuma ba su amsa kan abubuwan da suka shige masu duhu dangane da tsare-tsaren CBN.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *