Yaƙi da Cin Hanci Ba Lamari ne na Siyasa Ba — Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta yi watsi da zargin da wasu ‘yan adawa suka yi cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na amfani da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) a matsayin makamin siyasa, tana mai cewa hukumar mai zaman kanta ce da ke aiki bisa tanadin doka.

A cikin wata sanarwa da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara ta Musamman kan labarai, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Lahadi, fadar ta ce shugaba ƙasa ba ya bayar da umarni ga kowace hukumar yaƙi da cin hanci kan wanda za a bincika ko a gurfanar.

Sanarwar ta zo ne bayan wani taron da wasu fitattun ‘yan siyasar adawa suka gudanar, inda suka yi zargin cewa shigar manyan ‘yan siyasa jam’iyyar APC mai mulki na barazana ga dimokuraɗiyyar jam’iyyu da dama a ƙasar.

Fadar Shugaban Ƙasa ta ce kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ba wa ‘yan ƙasa ‘yancin shiga ko ficewa daga kowace jam’iyyar siyasa a duk lokacin da suka ga dama, tana mai cewa babu wanda aka tilasta masa shiga APC.

Ta ƙara da cewa masu sauya sheƙa suna yin hakan ne bisa ra’ayinsu, tare da ganin abin da ta kira nasarorin shirye-shiryen gyaran tattalin arziki da siyasa da gwamnatin Shugaba Tinubu ke aiwatarwa.

Game da binciken EFCC, fadar ta ce aikin hukumar shi ne bincike da gurfanar da duk wanda ake zargi da laifukan kuɗi, ba tare da la’akari da jam’iyyarsa ko matsayinsa ba.

Sanarwar ta ce abin lura ne yadda wasu daga cikin masu zargin gwamnati su ne ke adawa da bincike kan yadda aka tafiyar da kuɗaɗen jama’a a lokacin da suke kan mulki.

Ta kuma jaddada cewa EFCC na da cikakken ‘yancin aiwatar da aikinta, inda ta ce sakamakon ayyukan hukumar ne ya taimaka wajen fitar da Nijeriya daga jerin ƙasashen da Hukumar FATF ke saka ido a kansu.

Fadar Shugaban Ƙasa ta ce wasu daga cikin masu sa hannu a sanarwar adawa an riga an bincike su ko an gurfanar da su tun kafin Shugaba Tinubu ya hau mulki a 2023, yayin da wasu kuma suka faɗo a binciken kuɗaɗe na ƙasa da ƙasa.

A ƙarshe, fadar ta yi kira ga ‘yan siyasa da su daina amfani da siyasa wajen guje wa alhakin doka, tana mai cewa yaƙi da cin hanci ba batun jam’iyya ba ne, illa nauyin da ya rataya a wuyan kowa.

Sanarwar ta jaddada cewa babu wanda ya fi ƙarfin doka a Najeriya, kuma duk wanda ake zargi yana da ‘yancin kare kansa a gaban kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *