Daga Yusuf Kabiru
Tsohon jami’in leƙen asirin Amurka, John Stockwell ya bayyana yadda suke kifar da gwamnatocin ƙasashe tattare da juya su .

Ga abin da ya ce: “Mun shiga aikin kifar da gwamnatocin dimokiraɗiyya na tsarin mulki a fiye da ƙasashe 20. Mun yi maguɗin zaɓe a ƙasashe da dama. Mun kuma shirya ƙananan ƙabilu tare da ƙarfafa su su tayar da bore a ƙasashensu. Wannan dabara ce da CIA ta yi amfani da ita a Nicaragua, Thailand, Vietnam, Laos, Congo, da Iran da Iraƙ, da kuma a wurare daban-daban na duniya.’”
