YADDA MU’UTAMAR NA MANYAN ƊALIBAN FUDIYYA (FOSA), 2025. YA GUDANA A KADUNA

Daga Hafiz Nura Alja’afaree Roni.

Dandalin manyan Ɗaliban Fudiyya (FOSA) sun gudanar da gagarumin Mu’utamar na kwanaki uku cikin nasara da tsari a muhallin Makarantar Imam Sadiq (as) da ke Nassarawa, Kaduna. Taron ya tattaro manyan ɗalibai fudiyya daga sassa daban-daban na ƙasa domin tattauna muhimman batutuwa da suka shafi ilimi, tarbiyya, Inganta Fudiyyoyi da al’amarin haɓaka ilmi a cikin Harkar Musulunci.

Mu’utamar ɗin an fara shi ne a ranar Laraba 24 ga Disamba, 2025 (4 Rajab 1447H) da rajistar mahalarta. Daga bisani aka buɗe taron da karatun Alƙur’ani mai girma da addu’a.
An gudanar da jerin jawaban ilmantarwa da nasiha, tare da jaddada muhimmancin Fudiyya da Fudiyyanci.

A rana ta 2, an ci gaba da shirye-shirye tun daga safiya inda aka buɗe taron da addu’a da karatun Alƙur’ani. Malama Hauwa ta gabatar da ƙasida mai taken “Yadda ɗan Fudiyya Ya Kamata Ya Kasance: Darasi Daga Rayuwar Shehu Usman Dan Fodiyo (RA)”, in da ta bayyana darussan tarbiyya da tsayuwa kan gaskiya daga rayuwar Shehu Usman ɗan Fodiye (R).


Daga bisani Malam Muhammad Dauda ya yi jawabi kan “Hanyar yaɗa Labarai a matsayin makami; Yadda ya amata a yi amfani da Social Media”, inda ya ja hankalin mahalarta kan amfani da kafafen sada zumunta wajen yada ilimi da gyaran al’umma.


Malam S. Maina ya taɓo batun “Tabarbarewar makarantunmu; Gudummawar da ya kamata FOSA za su Bayar”, yayin da Dr. Nasir Hashim (KASU) ya yi jawabi kan “Tasirin Amfani da Hankali da Ilimi Wajen Sauya Al’umma”.


An kuma gudanar da zaman tattaunawa kan hulɗa da zamantakewa a addini, inda masana daga FOSA suka tattauna rawar da ɗan Fudiyya zai taka wajen kawo sauyi a cikin al’umma. Masu tattaunawar sun haɗa da Malam Ishaƙ Yunus Kaduna, Dr. Anas Abubakar Azare, Malama Walida Musa Azare da Malama Walida Sokoto.
Bayan kammala wannan tattaunawa, daga bisani, an gudanar da wani sashen tattaunawa da aka kira da “Muryar FOSA”, inda wakilan kwamitoci da na da’irarori suka gabatar da rahoton nasarorin da suka cimma a cikin shekara guda, kafin a rufe aana ta 2 da addu’a.

Rana ta 3, Juma’a 26/12/2025 ita ce ranar rufewa, inda Malam Zaharaddeen Katsina ya sake jaddada manufofi da muradun FOSA, sannan Malam Saminu Muhammad ya gabatar da jawabi kan “Hadafin Samar da Fudiyya a Jiya, Yau da Kuma Gobe.”
A ƙarshe, Sheikh Aliyu Tirmidhi Kaduna ne ya gabatar da Jawabin rufewa, tare da yin addu’o’i da nasiha ga mahalarta. Daga nan aka sallami ‘yan uwa, inda aka kawo ƙarshen mu’utamar cikin nasara da kwanciyar hankali.

Mu’utamar na FOSA ya kasance wata babbar dama ta ilmantarwa, haɗin kai da tantance hanyoyin da za su ƙara inganta ilimi da tarbiyya a cikin Harkar musulunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *