Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 58 tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, abin da gwamnatin jihar ta ce ya zama wani muhimmin tarihi a tafiyar shugabancinsa. A ranar Litinin ne gwamnan ya jagoranci wannan zama na 58 a zauren majalisar da ke Fadar Gwamnati a…
