Harin sama na sojojin Najeriya ya hallaka gungun ‘yan bindiga 23 da ke ƙoƙarin tserewa bayan kai hari a Kano
Rundunar Haɗin Gwiwa (JTF) tare da goyon bayan sashen sama na Operation Fansan Yamma sun hallaka akalla ‘yan bindiga 23 da ke ƙoƙarin tserewa daga Jihar Kano bayan kai hare-hare a ƙananan hukumomin Shanono da Tsanyawa. Wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Soja, Birgedi na 3 na Rundunar Sojin Nijeriya, Manjo Zubairu…
