Ba da yawu na Sa’idu Enagi ya yi rubutu kan siyasar Neja ba, kuma na dakatar da shi – Ministan Yaɗa Labarai
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa ba da yawun sa wani hadimin sa mai suna Sa’idu Enagi ya yi wani rubutu kan siyasar Jihar Neja ba. Shi dai Enagi, ya wallafa sharhin ne a kafafen yaɗa labarai da taken “Malagi 2027”, inda ya yi wani hasashe kan wasu…
